fidelitybank

Ƴansanda sun kama Mutane 1,254 da suka aikata laifi cikin shekara guda a Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane 1,254 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, sata, barna da sauransu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP. AT. Abdullahi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai nasarorin da rundunar ta samu a shekarar 2024.

A cewarsa, an kama mutane 1,254 bisa manyan laifuka daga ranar 20 ga Nuwamba, 2023 zuwa yau.

“Mutane tamanin da takwas (88) da ake zargi da yin fashi da makami, da masu garkuwa da mutane goma sha tara (19), wadanda ake zargi da aikata laifin fyade dari da ashirin (120) da kuma dari da hamsin da takwas (158) da ake zargin sun aikata laifin kisan kai.

“Sauran sun hada da, mutane dari takwas da sittin da tara (869) da ake zargi da aikata wasu laifuka kamar: Barna, Satar Shanu, Satar Dabbobi, Satar Muggan Kwayoyi, Satar Babura, Satar Motoci da Zamba.

“An kwato bindigogi goma sha bakwai (17), da suka hada da guda uku (3) AK-47, Bidistol daya (1), Bindigogin Dane guda goma (10), bindigu na gida guda uku (3) da kuma harsasai guda hamsin da hudu (54).” Yace.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce rundunar ta aiwatar da sabbin dabarun tunkarar kalubalen tsaro da suka kunno kai, da inganta hadin gwiwar al’umma, da inganta jin dadin jama’a da horar da jami’ai da maza.

Ya bukaci mazauna yankin da su marawa rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro goyon baya a kokarinsu na ganin jihar Jigawa da Najeriya ta samu zaman lafiya.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp