Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri’ar amincewa da hana mallakar bindiga kamar kananan bindigogin da akai amfani da su a hare-haren baya-bayan nan a kasar.
‘Yan jam’iyyar Democrat a majalisar sun amince da hanin mallakar, yayin da mafi yawancin ‘yan Republican suka ki amincewa.
A yanzu kudurin dokar zai wuce gaban majalisar dattawan kasar inda ake ganin da wuya kudurin ya kai labari.
Jam’iyyar Democrat a kasar ta jima tana kokarin ganin an sabunta kudurin mallakar bindiga a kasar wanda ya daina aiki tun 2004. A rahoton BBC.
To amma jam’iyyar Republican na ja a kan hakan tana mai cewa gyaran kundun tsarin mulkin kasar da aka yi ya bada dama ga ‘yan kasar a kan su mallaki makamai.