fidelitybank

Ƴan takara ku yi taka tsantsan a lamarin ku – Jonathan

Date:

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci ‘yan takara da kuma sauran ‘yan siyasa a kan su rika taka-tsantsan a kan dorewar kasa da kuma sanya jin dadi da walwalar al’ummar kasar a gaba a yayin yaki neman zabe.

Goodluck Jonathan, ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis a wajen taron shekara-shekara kan irin tariin da tsohon shugaban mulkin sojan kasar Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa.

A cewarsa, yana da matukar muhimmanci ga ‘yan Najeriya su kawar da dukkan wasu bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa don zabar shugabannin da za su kawo sauyi a kasar.

Ya ce,” Zabuka masu zuwa suna da matukar muhimmanci wajen ci gaban mu, a don haka ne nake jan hankalin ‘yan siyasa da su rinka taka-tsantsan wajen hada kai da kuma samar da zaman lafiya a kasa.”

Jonathan, ya ce a wannan lokaci da ake ciki bai kamata mu rinka nuna halin ko in kula da abubuwa da suka dace mu mayar da hankali a kai ba, dole mu sanya a ran mu cewa zamu shiga a dama damu a cikin harkokin siyasa.Dole kuma mu wayar wa da sauran ‘yan uwanmu kai a kan muhimmancin kada kuri’a a lokacin zabe.

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp