fidelitybank

Ƴan Shi’a sun kashe Jami’an mu biyu tare da raunana wasu a Abuja – Ƴan Sanda

Date:

Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya, ta tabbatar da cewa jami’anta biyu sun mutu yayin da wasu uku a halin yanzu ba su san hayyacinsu ba, sakamakon harin da ‘yan kungiyar haramtacciyar Harkar Musulunci ta Najeriya, IMN, da aka fi sani da ‘Yan Shi’a suka kai.

DAILY POST ta rawaito cewa, kungiyar Shi’ar ta kai hari kan wasu jami’an rundunar ‘yan sanda a mahadar Wuse a ranar Lahadin da ta gabata.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Josephine Adeh ya fitar ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce ‘yan kungiyar sun kai hari ne a shingen binciken ‘yan sanda da ke dauke da adduna, da bama-bamai (bama-bamai da aka kera a cikin kwalabe da kananzir), da kuma wukake” wanda ya kai ga mutuwar wasu jami’an.

Hukumar ta ce tuni aka kama mutane da dama dangane da kisan.

“Yayin da aka kama mutane da dama, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan jami’an ‘yan sanda.

“Ya yi alkawarin kawo wadanda ke da hannu a ciki. A halin yanzu halin da ake ciki yana karkashin kulawa kuma an dawo da yanayin al’ada.

“Za a sanar da ƙarin ci gaba a lokacin da ya dace.”

guardian newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp