Rundunar ‘yan sanda a Legas ta ce ta kama kimanin mutum 400 da take zargi da aikata ayyukan bata-gari a sassan birnin, a watan Janairu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin wanda ya tabbatar wa kamfanin labarai nakasa NAN, ya ce sassan ‘yan sanda 25 ne suka aiwatar da aikin.
Hyundeyin ya ce ya zama dole su kaddamar da babban samame bisa la’akari da irin korafe-korafen da jama’a ke kai musu da kuma bayanan tsaro da suka tattara.
Ya kara da cewa za a ci gaba da aiwatar da irin wannan tsarin domin tabbatar da an kakkabe baragurbi daga birnin na Legas.