Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tarwatsa wata kungiyar ‘yan bindiga da ta yi kaurin suna a babban birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin wani Isa Dei-Dei.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce an kai harin ne a ranar Litinin, ya kai ga artabu tsakanin jami’an da ‘yan fashin da suka yi kisa.
A cewar sanarwar, an kashe fitaccen dan fashi Isa Dei-Dei a yayin fafatawar da aka yi da bindiga, yayin da sauran mambobin kungiyar suka yi nasarar tserewa da raunukan harbin bindiga.
Rundunar ta yi kira ga jama’a musamman ma’aikatan kiwon lafiya da su kara kaimi idan aka ga mara lafiya da raunin harbin bindiga.
“Don haka muna kira ga jama’a musamman ma’aikatan lafiya da su sanar da mu ga duk wanda aka gani da raunin harbin bindiga domin ci gaba da bincike,” inji shi.