Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara, ta ce jami’anta sun tarwatsa wani yunƙurin ƴan bindiga na kai hari a wani ƙauye da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe.
Haka nan jami’an sun samu nasarar hallaka ƴan bindigan guda biyu.
A cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar a jihar, Mohammed Shehu, ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, inda aka yi artabu tsakanin jami’an ƴan sandan da kuma maharan.
Karanta Wannan: NDLEA ta cafke hodar Iblis a cikin ƙwaroron roban
Sanarwar ta ce baya ga waɗanda aka kashe, wasu maharan sun tsira da munanan raunuka