fidelitybank

Ƴan sanda sun kama matar da ake zargi da kashe kishiyarta a Katsina

Date:

Ƴan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure da ake zargi da kashe kishiyarta.

Lamarin ya faru ne a bayan wata makarantar firamare ta Dadi da ke unguwar Sabon Gari, a ƙaramar hukumar Daura bayan da wata matsala ta cikin gida tsakanin matan auren biyu ta rikiɗe zuwa rikici mai muni da ya kai ga mutuwa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyanawa manema labarai abin da ya faru.

Sanarwar ta ce: “A ranar 24 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11 na dare ne ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari suka samu rahoto daga wani Nasir Yusuf, mijin matar, cewa ya dawo gida daga kasuwa ya tarar da matarsa ta farko mai suna Zainab Lawal tana kwance cikin jini, an caka mata wuƙa sau da dama.”

“Da samun rahoton, DPO na yankin tare da tawagar jami’ai suka garzaya wurin da abin ya faru, inda suka gaggauta kai matar zuwa asibitin koyarwa na tarayya da ke Daura domin ceto rayuwarta, amma likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarta.”

“A yayin bincike ne aka kama kishiyarta, Rabi’a Labaran, wadda suke zaune a gida ɗaya bisa zargin aikata kisan.” in ji sanarwar.

“Kishiyar dai ta amsa laifin cewa ita ta aikata kisan bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninsu da mamaciyar, wanda ya rikiɗe zuwa fada har ta kai ga wannan mummunan lamari” sanarwar ta ƙara da cewa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bello Shehu, ya gargaɗi jama’a da su nisanci tashin hankali a cikin gida da kuma gujewa ɗaukar doka a hannu.

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp