‘Yan Sandan Merseyside na bincikar dan kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo, wanda ake zargi ya fasa wayar dan kallo.
Wani bidiyo da yake yawo a kafar sada zumunta dauke da sako, ya nuna lokacin da ya kwada wayar da kasa, bayan da United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Everton.
Daga baya Ronaldo mai shekara 37 ya nemi afuwa a kafar sada zumunta.
‘Yan Sandan Merseside sun ce suna binciken ”rahoto kan zargin cin zarafi” da aka yi a filin Goodison Park ranar Asabar.
Jami’in da ke magana da yawun jami’an tsaro ya ce suna tattaunawa da Manchester United da kuma Everton kan lamarin.
”A lokacin da ‘yan wasan ke barin fili da misalin karfe 2.30, an yi rahoton cewar an ci zarafin wani yaro daga wajen wani dan wasa baki a lokacin da za su bar filin.”