Rundunar ‘yan sandan Kaduna, ta ce, jami’anta sun ceto wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Kachia da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Muhammed Jalige, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba.
A cewarsa, an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne a kusa da babban birnin Kaduna.
Ya ce, a ranar 25/5/2022 da misalin karfe 0930 mutane bakwai (dukansu mata) da aka bayyana sunayensu kamar haka Godiya James 30yrs, Beauty Mandela 23yrs, Elizabeth Markus 13yrs, Alheri Maichibi 13yrs, Lydia Iliya 6yrs, Bridget Obadiah 4yrs da Amama duk 3yrs Kauyen Goro dake karamar hukumar Kachia an gansu suna yawo cikin daji bayan kauyen Tsohon Gayan.