Ƴan sanda sun kama wani matashi Abdul’azizi mai kimanin shekaru 32 ya na fakewa da sana’ar sayar da kayan miya daga bisani kuma a ka tsinci gawarwakin mutane a cikin gidansa.
Rahotanni na cewa, matashin ɗan yankin Gezaws ne, amma tun ya na ƙarami aka kawo shi Almajiranta cikin garin Dawakin Kudu, wanda kuma ya girma ya kama sana’ar sayar da kayan miya.
Lamarin da ya fara jawo a ka fara jin warin gawa a maƙotansa, wanda bincike ya yi nisa a ka shiga aka buɗe sai aka tarar da gawar wani Dattijo da ya ɓata kusan shekara guda ana nemansa.
Rahotanni na kuma cewa, jin haka ne mazauna yankin suka shiga cikin gidan tare da mahukunta aka kuma tona wani tudun ƙasa, sai ga shi an tono gawarwakin mutane wanda su ma suka ruɓe sai ƙasusuwa da kalar kayan jikin su, wanda aka ce suma tun tuni sun daɗe da ɓata a na ta cigiyar su har an haƙura.
Rahotanni sun ce tuni aka kai gawar mutum ɗaya asibiti sauran ƙasusuwan aka binne su, tare da sa hannun mahukunta, shi kuma matashin an tafi da shi domin ci gaba da bincike a kansa kuma kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar Kano ba ta magantu ba a kansa sai nan gaba.


