Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wata mata mai suna, Bola Agbedimu, mai shekaru 30, a ranar masoya, da ake zargin ta yi bushasha da kudaden jabu na Naira.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ya ce, an kama matar ne da takardun Naira 1,000 na jabu a kasuwar Kila da ke ƙaramar hukumar Odeda a jihar Ogun.
Jami’in ya ce, sun kama ta ne bayan samun rahoton cewa, ta na kashe kuɗin jabu a kasuwar, kuma nan take jami’an ƴan sanda suka yi mata dirar mikiya. A cewar BBC.
Ƴan sandan sun ce, sun samu kudi na jabu Naira 24,000a cikin jakar matar.
Sanarwar ta ce, bayan kammala bincike za a hukunta matar.