Tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce ‘yan ƙasa suna kewar mulkin jam’iyyar PDP na tsawon shekara 16.
Babangida Aliyu, ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta mika wa Alhaji Atiku Abubakar shaidar zama dan takarar ta a zabe mai zuwa.
Atiku Abubakar ya ce, ya daura damarar fara yakin neman zabe, domin tabbatar da karbe ragamar Najeriya a 2023.
A tattaunawarsa da BBC, Mu’azu Babangida Aliyu, wanda shi ne shugaban tsofaffin gwamnonin jam’iyyar ta PDP, ya bayyana shirinsu na tunkarar zaben badi.