fidelitybank

Ƴan Najeriya na cikin mawuyacin hali a Ukraine

Date:

Wasu dalibai ‘yan Najeriya da suka makale a birni Kherson na Ukraine wanda sojojin Rasha suka yi wa kofar rago sun bayyana mawuyacin halin da suka fada bayan mako biyu suna buya a wani dakin karkashin kasa.

Daliban na bukatar kasarsu ta dauki matakin ceto su da gaggawa.

Jerry Kenny ya shaida wa BBC cewa, shi da wasu abokansa shida ba su da lafiya, saboda mummunan halin da suke rayuwa cikinsa a dakin karkashin kasa, kuma ya ce ba su da abinci da sauran abubuwan more rayuwa.

“Wasu cikinmu ma ba sa iya magana saboda fargaba,” inji shi, kuma ya ce gwamnatin Najeriya “ba ta tuntube mu ba da zummar samar mana da ruwa da abinci”.

“Na yi magana da wakilan kasarmu da jakadu da kuma jami’an ma’aikatar harkokin waje kan yadda za a iya kwashe mu daga nan. Amma har yanzu babu labari.”

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce, ya tuntubi jakadun Najeriya da ke Ukraine da Rasha, kuma sun tuntubi takwarorinsu na Rasha da na Indiya, domin samar da hanyoyin kwaso daliban daga Ukraine zuwa Najeriya.

Rahotanni na cewa har yanzu akwai daliban nahiyar Afirka fiye da 100, yawancinsu daga Najeriya da ke Kherson.

daily post news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp