Rahotanni daga ƙasar Gambia sun ce, hukumomin ƙasar sun kama wasu mutum 13 da ke damfarar mutane ta intanet.
Mutum 12 daga cikinsu ƴan Najeriya ne, ɗaya kuma mutumin Saliyo, kamar yadda kafar yaɗa labarai a Fatu Radio ta ruwaito.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ne ta kama mutanen a Old Yundum da ke yankin yammacin Gambia, kamar yadda rahotanni suka bayyana.