Babban Editan Kundin Kafa Tarihi na Duniya, Guinness World Records Craig Glenday, ya shaida wa BBC cewa kundin ya samu takardun neman buƙatar kafa tarihi daga ‘yan Najeriya 1, 572 a yunƙurinsu na kafa tarihi tun bayan tarihin daɗewa a girki da Hilda Bachi ta kafa.
Mista Glenday ya kuma shawarci mutane da su riƙa yin rajista da kundin tare da bin sharuɗansa kafin fara yunƙurin kafa tarihin.
Kundin na Guinness ya kuma ƙarfafa wa ‘yan Afirka gwiwa wajen koyi da Hilda Bachi a fannin kafa tarihi.
Tun bayan kafa tarihin Hilda mutane da dama ne suka yi yunƙurin kafa tarihi a wasu fannoni daban-daban daga nahiyar Afirka.
An samu wanda ya yi yunkurin kafa tarihin kuka mafi tsawo, da mai suyan dodon koɗi da sauran abubuwa duk a yunkurinsu na kafa tarihi.
“Ina son ganin mutane na yunƙurin kafa tarihi” in ji mista Glenday.
“Haƙiƙa muna so ganin mutanen Afirka a fagen kafa tarihi, saboda abu ne mai kyau.”
Haka kuma ya ƙara da cewa kundin tarihin na Guinness na so a sanar da shi tun da fari, kafin a yi yunƙurin kafa tarihin, domin ya samu damar auna tarihin da ake son kafawar, ta hanyar bin sharudan kundin.
Mista Glenday ya ce kundin tarihin na yin watsi da kaso 95 cikin 100 na tarihin da aka yi yunkurin kafawa, sakamakon rashin bin ka’idojin kundin