Ƴan majalisar dokokin Kano guda biyu da suka haɗa da Kabiru Yusuf Isma’il wakilin mai wakiltar Madobi da kuma Mu’azzam El-Yakub, mai wakiltar ƙaramar hukumar Dawakin Kudu sun fice daga sabuwar jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari zuwa jam’iyyar APC.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar da safiyar yau Laraba ta ce ta tabbatar da rahoton sauyin sheƙar tasu.
A kwanakin baya ne dai ɗan majalisar dokokin Kano mai wakiltar ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono Ali Isah Shanono ya bayyana komawarsa APC kwanaki kaɗan bayan ya koma jam’iyyar NNPP,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Shi ma ɗan majalisar dokokin mai wakiltar Dambatta, Murtala Musa Kore, ya yi kome jam’iyyar APC mai mulki bayan da ya koma NNPP a baya. In ji Kakaki.