Ƴan fashin dajin da suka sace gomman yara da mata a ƙauyen Wanzamai na jihar Zamfara sun nemi a biya kuɗin fansa.
Iyaye da dangin waɗanda aka yi garkuwar da su, sun shaida wa BBC cewa a ranar Alhamis ne aka sace aƙalla mutum 90 lokacin da suke daji da kuma aiki a gonakin bayan gari.
Wata majiya ta ambato wani shaida daga Wanzamai yana cewa a cikin waɗanda aka sace har da fiye da mutum 20 daga ƙauyuka maƙwabta.
Hukumomin jihar Zamfara har yanzu ba su ce uffan ba kan rahotannin sace waɗannan yara da mata na ƙauyen Wanzamai.