fidelitybank

Ƴan Boko Haram sun kashe manoma huɗu a Borno

Date:

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP ne, sun kashe manoma akalla hudu a yankin Kerawa da ke kan iyaka a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

An ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis tsakanin karfe 12 zuwa 1 na rana a yayin da manoman ke aikin gonakinsu.

Wannan na zuwa ne kawai watanni biyu bayan da wasu bama-bamai suka hallaka sama da mutane 30 a garin Gwoza.

Mai ba da shawara na gundumar Jimini, Bukar Aji da shugaban kungiyar al’ummar Kerawa Yakubu Ali, sun tabbatar da faruwar lamarin.

Jaridar DAILY POST ta bayar da rahoton cewa, garin Kerawa na kan iyaka da kasar Kamaru a tsaunin Mandara, inda aka san ‘yan ta’addan na buya.

A halin da ake ciki, jami’in ‘yan sanda na shiyya ta Gwoza ya ce bai san da faruwar lamarin ba, inda ya yi alkawarin tabbatar da rahoton.

DPO ya ce harin na iya kasancewa daga Kerawa ne na kasar Kamaru, ba wai Kerawa na Najeriya ba, ya kara da cewa an yi irin wannan kisan a wasu makonni baya a garin Kerawa na kasar Kamaru, amma jama’a sun rikitar da yankin Kerawa na Najeriya.

DAILY POST ta tuna cewa an taba ayyana Gwoza a matsayin halifancin ‘yan ta’adda a lokacin da aka kama ta a shekarar 2014, kafin daga bisani dakarun sojojin Najeriya su kwato su.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp