Wasu da ake zargin ‘yanbindiga ne sun ƙwace iko da garin Bomborokuy da ke lardin Kossi a yammacin Burkina Faso, kamar yadda jaridar Info ta ruwaito.
A cikin wani bidiyo da jaridar ta wallafa a shafinta na X, an ga wasu mutum biyar sanye da kakin soja suna harba bindigogi suna magana da yaren yankin.
“Ƙungiyar ‘yanbindiga da ke dauke da makamai sun ayyana karɓe iko da Bomborokuy tare da ƙalubalantar shugaban mulkin soja Ibrahim Traore da ya kwato garin,” a cewar rahoton.
Shafin Wamaps ya ruwaito cewa, an kashe aƙalla fararen hula 20 a yankin ranar 12 ga watan Yuli tare da yin kaca-kaca da wata tasha ta tsaro da wasu dakarun sa-kai na gwamnati mai suna VDP ke kula da ita.
An kashe wani jami’in VDP ɗaya sannan aka jikkata wasu huɗu, a cewar shafin.


