Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, a daren Juma’a, sun kona gidan iyayen Kofoworola Babajide a Ede.
Babajide shi ne shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Osun.
An kuma tattaro cewa, mazauna garin na Ede yanzu haka suna cikin fargaba sakamakon afkuwar lamarin.
Babajide, yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar ya bayyana cewa ba a ga mahaifinsa ba tun lokacin da aka kona gidansa.
Ya bayyana cewa kafin a kona gidan iyayensa, tun da farko wasu ‘yan daba da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kai hari ga wasu ‘yan jam’iyyar PDP a wani unguwa da ya halarta a Ede.