fidelitybank

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutane lokacin da suke sallar Magariba

Date:

Akalla mutane 14 ne aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari a wani masallaci da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Rahotonni sun ce, daya daga cikin masu ibadar, Alhaji Buhari Nadama, wanda ya ce da kyar ya tsere, ya bayyana cewa, sun ji karar harbe-harbe a lokacin da suke sallar magariba.

Ya ce, bayan mintuna kadan, sai suka ga wasu mutane da suka rufe fuska, wadanda ke dauke da makamai.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun kuma tafi da wasu shanu daga wata unguwar da ke kusa da su, Tudun Amada.

Har ila yau, wani shugaban al’ummar yankin, Alhaji Dauda Mustapha ya bayyana cewa, yayin da wasu ‘yan ta’addan ke gudanar da ayyukansu a cikin masallacin, wasu kuma sun binciki gidaje da dama, inda suka dauko mata.

Sai dai wani mazaunin garin ya shaidawa kafar yada labarai cewa, an sako hudu daga cikin wadanda aka sace a daren Juma’a.

A halin yanzu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige bai tabbatar da faruwar lamarin ba.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp