Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sako tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Onje Gye-Wado, bayan sace shi da suka yi a ranar Juma’a.
Mai magana da yawuyn rundunar ƴan sanda a jihar, Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan ga manema labaru a ranar Litinin.
Nansel ya ce, tsohon mataimakin gwamnan ya kwashe kwana biyu a hannun ƴan bindiga, waɗanda suka sako shi a cikin dare, ranar Lahadi, bayan matsi daga jami’an ƴansanda masu neman inda yake.
Karanta Wannan: Ƴan Sanda sun raraki ƴan bindiga a Zamfara
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai wasu mahara suka yi awon-gaba da Gye-Wado bayan kutsawa cikin gidansa da ke ƙauyen Gwagi a jihar ta Nasarawa.
Inda daga baya jami’an tsaro suka ce sun bazama domin gano inda ake garkuwa da shi.