‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mambobin kungiyar Makiyaya ta (MACBAN) su 10 tare da sace shanu 300 a jihar Anambra.
An kai wa Fulanin harin ne cikin dare suna bacci a Obene cikin ƙaramar hukumar Ogbaru a jihar Anambra, kamar yadda shugaban Miyetti Allah shiyar kudu maso gabashin Najeriya, Alhaji Gidado Siddiki ya shaida wa jaridar The Nation.
Ƴan bindigar da aka bayyana sun kai 40 ɗauke da manyan makamai sun buƙaci a biya su miliyan hudu a matsayin kuɗin fansa da kuma bindiga daga iyalan wadanda aka kama.