Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a ranar Litinin din da ta gabata, sun mamaye al’ummar Ojiogu da Okpochiri Ukwagba da ke karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi inda aka ce sun kashe wani dan asalin jihar tare da kona gidaje da dama.
An kuma ce, maharan sun yi awon gaba da ’yan asalin yankin da dama
An tattaro wannan ci gaban, ya sa wasu ‘yan asalin yankin da suka tsira daga harin suka fice daga cikin al’umma saboda fargabar kara mamayewa.
Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunanta saboda wasu dalilai, ta ce ,‘yan bindigar sun kutsa kai cikin al’ummar, inda suka yi ta harbe-harbe, inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Majiyar ta kuma tabbatar da cewa an kona gidaje da dama..
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya ce, har yanzu ba a yi wa rundunar bayanin faruwar lamarin ba.