fidelitybank

Ƴan bindiga sun kashe mutum 12 da ƙona gidaje a Neja

Date:

Rahotanni daga ƙaramar hukumar mulkin Shiroro a jihar Neja na cewa, wasu da ake zargin mayaƙan kungiyar Boko Haram ne sun kashe sama da mutum goma sha biyu tare da ƙona kimanin gidaje talatin a wasu jerin hare-hare da suka kai.

Mazauna yankunan sun ce hare-haren sun faru ne a tsawon makon da ya gabata, a garuruwan Alawa da Bangajiya da sauran su, inda baya ga kashe mutane da dama da maharan suka yi sun kuma yi awon gaba da dukiya mai ɗimbin yawa.

Wani Mazaunin garin ya shaida wa BBC cewar sama da makonni biyu ke nan suke fama da tashe tashen hankula na hare-haren ƴan bindiga waɗanda suka hana su sukuni.

A cewar sa, a makon da ya gabata ne ƴan bindigar suka dasa bam a hanya wanda ya tashi da wasu da ke kan hanyar komawa ƙauyukansu daga kasuwa kuma nan take mutane aƙalla takwas suka rasa rayukansu.

Da aka je kwashe gawawwakin waɗanda aka kashe kuma aka sake kai wani harin da ya yi sanadiyar asarar rayuka sannan suka hana daukar gawawwakin wanda har ya zuwa yanzu babu labarin kwashe gawawwakin.

Shugaban ƙaramar Hukumar Shiroro Hon. Akiku Kuta ya tabbatar da harin

Wadannan sabbin hare-haren dai sun sa mutane da dama yin hijira zuwa wasu makwabtan garuruwa

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp