A ranar Alhamis din da ta gabata ne ‘yan ta’adda suka kai hari a unguwar Rumache Madalla da ke unguwar Bassa/Kukoki, inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da mutane sama da 20 ciki har da wani shugaban al’umma, Malam JagwallaWassa.
Jaridar The Nation ta samu labarin cewa, an kai harin ne da misalin karfe 4 na Yammacin ranar Alhamis, yayin da ‘yan ta’addan suka mamaye al’umma da muggan makamai.
Wasu da dama sun samu raunuka a harbin bindiga, kuma a halin yanzu suna samun kulawa a wuraren kiwon lafiya.
‘Yan ta’addan sun kuma lalata shaguna da da gidaje. Sun kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.
Kiran da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ya ci tura.