Akalla mutane biyar ne aka kashe tare da yin awon gaba da daruruwan shanu a wasu hare-hare guda biyu da aka kai a kauyukan Shegyam da Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Wase na jihar Filato a arewa ta tsakiyar Najeriya.
Politics Nigeria ta samu labarin cewa, wasu gungun miyagu da aka fi sani da ‘yan bindiga ne suka kai harin da sanyin safiyar Laraba.
‘Yan bindigar sun kai hari Shegyam, inda ‘yan ta’addan suka kashe mutum biyu sannan suka wuce Dogon Ruwa, inda suka kashe wasu mutane uku tare da yin awon gaba da daruruwan shanu.
‘Yan sanda jihar Filato sun tabbatar da faruwar lamarin.
Jihar Filato dai tana kan iyaka da jihar Kaduna, inda a halin yanzu ke zama mafakar ‘yan fashi.