Yan Fashin daji sun kashe dakarun rundunar tsaro a jihar Zamfara 10 a wani kwanton ɓauna da suka yi musu ranar Asabar.
Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ce shida daga ciki dakarun tsaron gwamnatin jihar ne da ake kira Askarawa, huɗu kuma ‘yan sa-kai ne.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya ƙara da cewa akwai dakarun Asakarawa biyu da ɗan sa-kai ɗaya da suka ɓata.
“Lamarin ya faru ne bayan farmakin da gamayyar jami’an tsaro [ciki har da Askarawa] ƙarƙashin jagorancin sojojin Najeriya suka kai wa sansanin ‘yanbindiga a Dajin Sunƙe, wanda aka samu gagarumar nasarar kashe da dama tare da ƙwato makamai masu tarin yawa,” in ji Gwamna Lawal.
Ya ce tuni aka yi jana’izarsu a yau Lahadi, yana mai cewa ya bayar da umarnin ɗaukar “matakin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka ji raunuka” da kuma “bayar da tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasu”.