Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, a ranar Alhamis da daddare, suka kai farmaki kauyen Koro, a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, sun kashe sarkin al’ummar, Olukoro na Koro, Janar Segun Aremu, (mai ritaya) tare da sace matarsa, tare da wasu mutane biyu.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi Allah wadai da kisan Olukoro na Koro, yana mai bayyana lamarin a matsayin rashin hankali, abin ban tsoro da kuma abin kyama.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da kada su yi kasa a gwiwa wajen zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika, a sako matar da sauran wadanda aka kama, tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
“Tabbas za mu samu wadanda suka aikata laifin kuma mu tabbatar da cewa wannan shi ne laifinsu na karshe na cin zarafin bil’adama,” in ji Gwamnan, ya kara da cewa: “Ina mika ta’aziyyata ga mutanen Koro.”