Ƴan bindiga sun kai hari karamar hukumar Kankia na jihar Katsina tare da kashe mutum ɗaya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ƴan bindigar sun harbi mutumin ne lokacin da suka kai hari wani rukunin gidaje da ke unguwar low-cost kusa da babban asibitin karamar hukumar a daren Asabar.
Wani ganau ya bayyana cewa ƴan bindigar sun zo ne a kan babura, inda suka yi wa rukunin gidajen dirar miƙiya tare da harbi kan mai uwa da wabi, abin da kuma ya janyo mutuwar mutumin mai suna Alhaji Ibrahim Baraya Solo.
Bayan kashe mutumin ne, sai maharan suka tsere tare da barinsa cikin jini.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni ƴan sanda suka fara bincike kan lamarin domin kamo waɗanda ke da hannu a kai harin.