Masarautar Sabon Birnin Gobir a jihar Sakkwato ta tabbatar sako dan marigayi Sarkin Gobir Alhaji Muhammad Bawa Isa da aka sace su tare mai suna Kabiru.
Wani mai magana da yawun masarautar Alhaji Shuaibu Gwanda Gobir ya ce an sako shi ne da daren jiya bayan biyan wadanda suka yi garkuwa da shi da kuma mahaifinsa kudin fansar da suka bukata, amma sun ki bayar da gawar mahaifinsa inda suka ce sun riga sun binne shi.
Yanzu haka dai dan nasa na can na karbar magani a asibiti a birnin Sakkwato. Magajin Garin na Sabon Birni ya ce za su yi wa marigayi Sarkin Gobir jana’iza daga nesa wato salatul Ga’ib a yau.
Ya bukaci al’ummar Musulmi a duk duniya da su bi sawunsu wajen yi masa sallar wadda ya ce za su yau.