Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da sakin yara 21 da ‘yan bindiga suka sace a yayin da suke aikin gona a unguwar Mairuwa da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata ‘yar gajeruwar sanarwa da ya fitar a daren Asabar.
A cewarsa, wadanda aka saki da suka hada da ‘yan mata 17 da maza hudu daga an mika su ga iyalansu yayin da ake ci gaba da bincike.