Gwamnatin Isra’ila ta ce ƴan Tanzaniya biyu da ɗan Afirka ta Kudu na daga cikin mutane 224 da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su bayan harin ranar 7 ga Oktoba.
Babu sunan ko ɗaya daga cikin ukun da aka ambata.
Hukumomin Tanzaniya a baya sun tabbatar da cewa wasu ƴan ƙasarta biyu sun bata.
BBC ta tattauna da dangin ɗaya daga cikinsu, Joshua Mollel, wanda ɗalibi ne a fannin aikin gona a wani kibbutz da aka kai masa hari.
Ƴan ƙasashen waje daga ƙasashe 25 gaba ɗaya na hannun Hamas, in ji Isra’ila.
Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani da hare-hare ta sama kan Gaza, wanda ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce ta kashe kusan mutum 6,500.


