Shugaban Amurka Joe Biden ya dage kan cewa shi ne mutum mafi cancanta da zai jagoranci kasar.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan wani bincike da ya gano cewa ya yi sakaci kan wasu manyan bayanan sirri tare da danganta hakan ga matsalar shugaban ta kasa tuno abubuwa.
A wajen wani taron manema labarai da ya kira, shugaba Biden ya ce ƙwaƙwalwarsa lafiya lau take inda ya yi kakkausar suka ga mai binciken.
“Ya kafa hujja da cewa ba na iya tuno lokacin da ɗana ya mutu, waye shi da zai ce haka? bani buƙatar sai wani ya tuna mani da lokacin da ɗana ya mutu,” in ji Shugaba Biden na Amurka