Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya caccaki ‘yan wasansa, bayan da suka sha kashi da ci 4-2 a karawar da suka yi da Girona ta Catalan a gasar La Liga ranar Talata.
Kwallaye hudu da Valentin Castellanos ya ci ne suka tabbatar Girona ta doke Real Madrid a Montilivi.
Vinicius da Lucas Vazquez ne suka ci wa Real Madrid kwallaye a karawar.
Da yake mayar da martani, Ancelotti ya ce, a taron manema labarai na bayan wasan da Real Madrid ta buga da Girona ya yi karanci, inda ya kara da cewa ‘yan wasansa sun kare da kyar kuma ba su yi wasa da mai masaukin baki ba.
“Matakinmu ya yi ƙasa sosai. Muna ba da hakuri, kungiyar ba ta buga komai ba,” in ji Ancelotti.
“Mun kasance marasa kyau na tsaro kuma wannan shine mabuɗin shan kashi. Mun kasance cikin damuwa kuma mun dogara ga wasa ɗaya.
“Su (magoya bayan Real Madrid) za su ji rauni da fushi kamar mu.
“Amma muna bukatar mu tuna cewa muna cikin gasar cin kofin zakarun Turai kuma a wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai,” in ji shi.