Hukumar lafiya ta Duniya (WHO), ta ce, kimanin mutum 922 ne aka bayyana cewa, sun kamu da cutar kwalara ko amai da gudawa a Najeriya, yayin da mutum 32 suka mutu sakamon cutar a shakerar 2023 da muke ciki.
A wani rahoton da WHO ta fitar, ta ce, zuwa 5 ga watan Maris 2023 yawan mace-mace sakamakon cutar ya kai kashi 3.5 cikin 100
WHO ɗin ta kuma ce, alƙaluman sun haɗar da waɗanda suka bayyana alamun cutar, da kuma waɗanda aka tabbatar da cewa sun kamu a ɗakunan gwajin cutar da ke asibitocin ƙasar.
Ta kuma ce alƙaluman ka iya sauyawa a kowanne lokaci sakamakon rahotonnin da ake samu a mabambantan wurare a faɗin ƙasar.
Cutar Kwalara ko amai da gudawa, cuta ce da ake kamuwa da ita sakamakon ɗaukar ƙwayar cutar ‘cholerae bacteria’, mutum kan kamu da cutar idan ya ci abinci ko ya sha ruwan da ke ɗauke da ƙwayar cutar.
Cutar dai kan zo da tsanani wanda a wasu lokutan ma take barazana ga rayuwar wanda ya kamu da ita, matuƙar bai samu kulawar gaggawa ba.
A wani labarin na daban kuma wani rahoto da hukumar daƙile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta wallafa a shafinta na intanet, ya nuna cewa an tabbatar da samun mutum 157 da ke ɗauke da cutar sankarau tsakanin watan Oktoban bara zuwa watan Maris da muke ciki.
Haka kuma an samu marasa lafiya da ake zargin sun kamu da cutar su kusan 628, ciki har da mutum 52 da suka mutu a jihohin ƙasar 21.
Alamomin cutar sun haɗar da zazzaɓi da ciwon kai da tashin zuciya da amai, da sanƙarewar wuya.