A yau ne ƙungiyoyin kwadago na zanga-zanga saboda tsadar rayuwar da al’umma ke fuskanta a ƙasar nan.
Ƙungiyar kwadagon ta ce za ta yi zanga-zangar ne na yini biyu – Talata da Laraba.
Hauhawar farashi a ƙasar wadda tattalin arzikinta shi ne mafi girma a Afirka ya kai kusan kashi 30 cikin 100 yayin da darajar naira ke ci gaba da karyewa.
Matsalar rashin wuta na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta’azzara halin matsin da ake ciki a ƙasar.
Bankin raya ƙasashen Afirka AfDB ya yi gargaɗin cewa halin da ake ciki na iya janyo bore a ƙasar duk da cewa tuni wasu jihohin ƙasar suka yi makamanciyar zanga-zangar ta tsadar rayuwa.
Gwamnati ta ce za ta rage kuɗin da take kashewa wajen tafiyar da harkokinta sannan ta yi alƙawarin ɗaukan matakai domin taimakawa al’umma da kuma masu ƙananan sana’oi.
Babu bayanai kan yawan ma’aikatan da za su shiga zanga-zangar saboda mutane da dama na zargin ƙungiyoyin da rashawa.