Ƙungiyar kamfen din Bola Tinubu, ta ce, ficewar babban daraktan yakin neman zabenta (DG) Alhaji Abdulmumin Jibrin daga jam’iyyar APC ba shi da alaka da Sen. Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Majiyar wadda ta zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN), bisa dalilai na kin amincewa, ta ce murabus din tsohon dan majalisar tarayya ba shi da wata alaka da Tinubu ko kuma Jibrin na aiki a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Kungiyar Tallafawa Tinubu.
Jibrin wanda ya wakilci mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano a shekarar 2015, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.
Sai dai kuma an tattaro cewa, Jibrin na cikin wani bangare na jam’iyyar APC a jihar Kano, karkashin jagorancin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, da suka sha kaye a kotun koli a ranar Juma’a a hannun bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje.