Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta bunkasa tallafin kudi ga Hukumar Falasdinu da wani kunshin shekaru uku na kusan Euro biliyan 1.6 (dala biliyan 1.8).
Kwamishinan Tarayyar Turai mai kula da tekun Mediterrenean Dubravka Suica, ya ce tallafin kudi zai tafi kafada da kafada da sauye-sauyen hukumar Falasdinu, wadda masu sukar almundahana da rashin gudanar da mulki ke zargi.
Suica ta ce “Muna son su gyara kansu domin ba tare da gyara ba, ba za su kasance masu karfi da gaskiya ba domin su zama masu shiga tsakani, ba don mu kadai ba, har ma da Isra’ila,” in ji Suica.
Wannan dai na zuwa ne gabanin wata babbar tattaunawa ta siyasa ta farko tsakanin ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai da manyan jami’an Falasdinawa ciki har da firaminista Mohammad Mustafa a Luxembourg ranar Litinin.
EU ita ce babbar mai ba da taimako ga Falasdinawan kuma jami’an EU na fatan hukumar Palasdinawa mai kula da gabar yammacin kogin Jordan, ita ma wata rana za ta iya daukar nauyin Gaza bayan an kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da mayakan Hamas.
Sai dai gwamnatin firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya zuwa yanzu, ta yi watsi da ra’ayin mika Gaza ga hukumar Falasdinu, tare da yin watsi da babban burin kungiyar EU na samar da kasashe biyu, wanda zai hada da kafa kasar Falasdinu.
A cewar Suica, Euro miliyan 620 za ta je ne ga tallafin kudi da yin gyare-gyare ga hukumar Falasdinu, da Euro miliyan 576 don jurewa da farfado da yankin yammacin kogin Jordan da Gaza da kuma Euro miliyan 400 za a samu lamuni daga bankin zuba jari na Turai, bisa amincewar hukumar gudanarwarta.
Ta kara da cewa matsakaita tallafin da EU ke baiwa hukumar Falasdinu ya kai kimanin Euro miliyan 400 cikin shekaru 12 da suka gabata.
Suica ta ce “Yanzu muna saka hannun jari cikin sahihiyar hanya a Hukumar Falasdinawa.”