Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), ta bi sahun kungiyoyin kwadago NLC da TUC a wani yajin aikin da suke yi a fadin kasar.
ASUU ta umarci mambobinta a ranar Litinin da su shiga yajin aikin da tsakar daren ranar Litinin.
Kungiyar ta fitar da wata takarda ce ga kodinetoci da shuwagabannin ta na shiyyar, wanda ya samu sa hannun Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar na kasa.
“A matsayinta na kungiyar NLC, ana umurtar dukkan mambobin kungiyar mu da su shiga wannan mataki na NLC domin kare muradun ma’aikatan Najeriya da kuma shugabannin kungiyar.
“Masu gudanarwa na shiyyar da shugabannin reshe ya kamata su gaggauta hada kan mambobinmu domin su shiga cikin wannan aiki.”
Platinumpost ta ruwaito cewa, NLC da TUC sun rubutawa kungiyoyinsu, inda suka umurce su da su fara yajin aikin da suka shirya yi a fadin kasar nan da aka shirya fara tsakar daren ranar Litinin.
Yajin aikin dai ya biyo bayan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero, da jami’an ‘yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Imo suka yi.


