Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’Adam ta duniya ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da ƴan bindiga suka kai jihar Zamfara inda suka sace ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau.
Darektan ƙungiyar a Najeriya, Mallam Isa Sanusi a tattaunawarsa da BBC ya ce, yadda ƴan bindiga ke jefa rayukan mutane cikin haɗari haka babban abin takaici ne da kuma ƙyama.
Ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya da dukkanin hukumomin da nauyi ya rataya a wuyansu su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan ta’asa da cin karen da ƴan bindigar ke yi babu babbaka.
Darektan ya ce, “wannan abin ya isa haka mutanen jihar Zamfara tura yanzu ta kai bango ya kamata a ceto su daga hannun waɗannan mutane waɗanda suke cutar da su suna kashe su sun hana su noma suna yi wa matansu fyaɗe suna yi wa ƴaƴansu fyaɗe yanzu kuma ga shi har suna hana yara makaranta.”