Tsohon tauraron wasan damben boxing, Myke Tyson, ya nannaushi wani fasinja a cikin jirgi sakamakon abin da ya ce robar ruwa da aka cilla masa.
Wani bidiyo da aka ɗauka a cikin jirgin ya nuna yadda Mista Tyson ya ragargaje mutumin yana kai masa naushi ba ƙaƙƙautawa a ka.
Sai dai kafin faruwar hakan, an ga wani matashi na tsaye ta bayan kujerar da Tyson ke zaune yana maganganu, kodayake ba a jin abin da yake cewa.
A cewar TMZ, Tyson ya amince ya ɗauki hoto da mutumin, amma kuma daga baya ya ci gaba da matsa masa duk da cewa ya nemi ya bari.
‘Yan sanda sun ce sun saki mutum biyun da suka tsare, amma za a ci gaba da bincike.