fidelitybank

Ƙasashen ECOWAS za su tattauna kan harajin ƙasashen yankin Sahel

Date:

Ƙungiyar ECOWAS za ta gudanar da taron na musamman domin tattaunawa kan harajin kayayyaki da ƙungiyar ƙasashen AES suka lafta wa ƙasashenta.

Ƙasashen ECOWAS za su zauna ne a watan da ake ciki na Afrilu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga jami’in watsa labarai na ƙungiyar ƙasashen Joel Ahofodji.

Ya ce, “za a yi taron ne a ranar 22 ga Afrilu kan harajin kashi 0.5 da ƙasashen AES suka lafta wa kayayyakin da ke shiga ƙasashensu da su daga ƙasashen ECOWAS.”

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar ƙungiyar ECOWAS ɗin za ta mayar da martani wajen ɗora wa ƙasashen na AES haraji, sai ya ce, “a lokacin taron za a tattauna komai da komai.”

Ƙasashen AES wato Mali da Nijar da Burkina Faso da suke ƙarƙashin mulkin soji ne suka sanar da ɗora wa ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da suka fice harajin kashi 0.5 kan kayayyakin da ake shiga da su, “domin samun kuɗaɗen shiga.”

Harajin zai fara aiki ne daga ranar 28 ga watan Maris, amma banda kayayyakin agaji.

Wannan ya saɓa da yadda aka saba na cinikayya da shiga da fitar da kayayyaki ba tare da shinge ba a tsakanin ƙasashen ECOWAS.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp