A yau Alhamis ne manyan hafsoshin soja daga ƙasashen da ke shirin kafa rundunar wanzar da zaman lafiya a Ukraine za su gana a Birtaniya.
Ana tsamanin ƙasashe fiye da 20 ne za su shiga cikin abinda Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya kira ”ƙawancen masu son su taimaka”.
Ana dai sa rai taron wanda zai gudana ƙarƙashin jagorancin Birtaniya da Faransa zai maida hanakali ne kan yadda rundunar wanzar da zaman lafiya ta ƙasashen yamma za ta gudanar da ayyukanta.
Shugaba Putin na Rasha dai ya ce ƙasarsa ba za ta amince da kasancewar dakarun kungiyar tsaro ta NATO a Ukarain ba