Wata Babbar jami’a a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sa ido kan agaji da sake gina Gaza ta ce duniya ta nuna gazawa wajen taimaka wa fararan hula kusan shekara guda na yaƙi.
Sigrid Kaag ta faɗa wa BBC cewa rahotan da take shirin gabatar wa kwamitin tsaro na Majalisar a yau Litinin na tattare da labaran ƙunci da tashin hankali.
An dai naɗa Sigrid Kaag wannan muƙamin ne watanni tara da suka gabata domin inganta yadda ake shigar da agaji Gaza.
Ta ce a yanzu komai ya tsaru, sai dai kuma ƙoƙarin kare ayarin motocin agaji ya gaza. Ms Kaag ta ce ba ta ganin za a samu wani sauyi a yanzu, indai ba tsagaita wuta aka yi ba.