Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana cewa, lokacin da zai tabbatar da cewa matsayin kasar Sin na kan hannun dama na tarihi a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine.
Wang Yi, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.
“Kasar Sin za ta ci gaba da yanke hukunci mai cin gashin kanta, bisa cancantar lamarin da kuma bisa gaskiya da adalci.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ba za mu taba amincewa da duk wani tilastawa da matsin lamba daga waje ba, kuma muna adawa da duk wani zargi da zato mara tushe kan kasar Sin.”
Wang ya ce, “Maganin dogon lokaci shi ne a yi watsi da tunanin yakin cacar-baki, da kaucewa shiga cikin fadace-fadacen kungiya, da samar da daidaito, inganci da dorewar gine-ginen tsaro na yankin. Ta haka ne kawai za a iya samun kwanciyar hankali na dogon lokaci a nahiyar Turai.”
Ku tuna cewa, yaki tsakanin Ukraine da Rasha ya fara ne a watan Fabrairu.
Yakin ya shiga kwana na ashirin da uku a yau, inda tuni aka samu asarar dimbin rayuka.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da umarnin mamaye kasar Ukraine, bisa rashin jituwa kan wasu batutuwan siyasa.
Putin ya kuma lissafa wasu sharuddan kawo karshen yakin.