Kevin de Bruyne ya tabbatar da cewa, zai bar Manchester City idan kwantiraginsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana.
De Bruyne, mai shekara 33, ya lashe kofuna 16 tun bayan komawa City daga Wolfsburg a 2015 – ciki har da kofin Premier shida da gasar zakarun Turai a 2023.
Ya zura kwallo 106 a wasanni 413 da ya buga wa ƙungiyar, sai dai an fara da shi a wasanni 19 kaɗai a bana.
“Komai yana da farko da kuma karshe, amma zama na a City ya kasance wani babi mafi kyau a rayuwata,” kamar yadda ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Belgium ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.