Ɗan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaɓen gwamnan jihar Kogi ya yi zargin cewa an yi maguɗi a zaɓen na ranar Asabar, yana mai cewa ba zai je kotu ba “saboda ɓata lokaci ne”.
Murtala Ajaka wanda ya zo na biyu a sakamakon da hukumar zaɓe Inec ta bayyana, ya faɗa wa kafar talabijin ta Channels TV cewa zuwa kotu ɓata lokaci ne “saboda hukumar zaɓen za ta je kotun kuma ta kare sakamakon da ta bayyana”.
Inec ta ce Usman Ododo na jam’iyyar APC ne ya yi nasara bayan ya samu ƙuri’a 446,237, sai Ajaka da ya samu 259,052, da kuma Dino Melaye na PDP mai ƙuri’a 46,362.
“Na shafe shekara 20 ina siyasa, saboda haka na san yadda lamarin yake. Me zan je kotu na yi bayan Inec ɗin da suka yi wannan abin za su je kotun a matsayin waɗanda ake ƙara kuma su kare abin da suka aikata?” in ji Ajaka.
“Wannan ɓata lokaci ne kawai, sai dai jam’iyya [ta kai ƙara] amma ni kam raina ya ɓaci sosai.”
Tun kafin a kammala tattara sakamakon zaɓen, ɗan takarar PDP Sanata Dino Melaye ya yi watsi da shi, yana mai neman Inec ta soke shi gaba ɗaya.