fidelitybank

Zulum zai sake gina ƙauyuka uku don mayar da ƴan gudun hijira

Date:

Gwamnamn jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana shirin sake gina wasu ƙauyuka uku domin sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da mayaƙan Boko Haram suka raba da muhallansu.

Fiye da mutum 20,000 ne boko haram ta raba da muhallansu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, waɗanda wasunsu ke zaune a makwabtan ƙasashen Nijar da kamaru da Chadi.

A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce, tun shekarar 2014 ne mayaƙan Boko Haram ta raba mutanen da muhallansu.

Zulum ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da kwamitin maido da ‘yan gudun hijirar da ke ƙasashen waje a Abuja babban birnin ƙasar. In ji BBC.

Gwaman Zulum shi ne mataimakin kwamitin shugaban ƙasa na maido da ‘yan gudun hijirar ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje , tare da sauya tunanin mutanen da da Boko Haram ta sako.

Inda mataimakin shugaban ƙasa farfesa Yemi Osinbajo ke zaman shugaban kwamitin.

Gwamna Zulum ya ce, shugaba Buhari ya amince da bai wa kwamitin naira biliyan 15, yayin da gwamnatin jihar Borno ke shirin sake gina ƙauyuka uku don tsugunar da ‘yan gudun hijirar.

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp